Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na Æ™asa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar gudanarwar Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN).
Wannan na cikin sanarwar da Aminu Dahiru Ahmad, mai kula da harkokin sadarwa ta bidiyo da gani da ido na Gandujen ya fitar a ranar Laraba, 9 ga Yuli, 2025.
Sanarwar ta ce Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ne ya jagoranci bikin kama aikin na Ganduje tare da ƙaddamar da sauran mambobin hukumar.
Tun a watan Janairu, 2025, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya naÉ—a Dr. Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban hukumar gudanarwar FAAN É—in.