Majalisar Malaman Kano za ta gudanar da Sallar rokon Ruwa a ranar Asabar mai zuwa
Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta shirya gudanar da Sallar roƙon ruwa a ranar Asabar mai zuwa 12 ga Yulin 2025 a Masallacin Dangi da ke birnin Kano.
Wannan na cikin sanarwar da Majalisar ta aike wa manema labarai mai É—auke da sa hannun Shugabanta Sheikh Ibrahim Khalil a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce za a gudanar da Sallar da karfe 9:00 na safe kamar yadda koyarwar Annabi Muhammad (SAW) ta tanada.
Majalisar ta bukaci al’umma da su halarta cikin nutsuwa da tsafta, tare da neman gafarar Allah da addu’ar samun ruwa.