Mutane 2,266 ƴan Bindiga suka Kashe a watanni 4 na shekarar 2025
Wasu sabbin alƙaluma da hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta fitar sun nuna yadda matsalar kashe-kashen ƴan bindiga ke kara tsananta a Najeriya. A cewar rahoton da aka fitar a ranar Talata, an kashe mutane 2,266 a watanni hudu na farkon shekarar 2025, abin da ya zarce adadin mutanen da aka kashe a duk shekarar da ta gabata.
Idan aka kwatanta, ƴan bindiga sun kashe mutane 1,083 a watanni hudu na farkon 2024, yayin da aka kashe 2,194 a gaba ɗaya shekarar ta 2024. Wannan na nuni da yadda hare-haren ke ƙaruwa duk da ƙoƙarin jami’an tsaro.
Sojojin Najeriya dai na fama da yaƙi a fannoni da dama – daga yakar ƴan bindiga, ƙungiyoyin Boko Haram da sauran mayaƙa a arewa maso gabas, zuwa yaƙi da masu satar mutane da rikicin makiyaya a arewa ta tsakiya, da kuma hare-haren ƴan aware a kudu maso gabas.
A shekarar da ta gabata ma, rahotanni sun nuna cewa mutum 606 ne aka kashe a hare-haren ƴan bindiga a wurare daban-daban, ciki har da ƙauyukan Yelwata da Dauda a jihar Benue, inda aka kashe kimanin mutane 200.
Da yake bayyana wannan rahoto a Abuja, babban sakataren hukumar kare haƙƙin ɗan Adam, Tony Njokwu, ya roƙi gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa don dakile wannan matsala. Ya ce waɗannan mutanen ba kawai alƙaluma ba ne, iyaye ne, ƴaƴa da masu kula da iyalai, waɗanda mutuwarsu ta lalata rayuwar waɗanda suka dogara da su.