Masu kasuwancin harkokin kayan kwalliya na "Custimetic" sun bayyana cewar hukumar kula da ingatattun kaya ta kasa "NAFDAC" na musu barazanar durkusar da harkokin kasuwancin su a Kano.
Wannan na zuwa ne lokacin da masu sana'ar sayar da kayan kwalliya suka shirya domin lalubu hanyar da yakamata su bi wajen kaucewa baranazar durkushewar kasuwanci a Kasuwa Sabon Gari dake Kano.
Shugaban kungiyar Alhaji Ibrahim Ikon Allah yace, "Muna tsaka da kasuwanci mu mukaga shigowar ma'aikatan NAFDAC da jami'an tsaro dauke da bindigu suna bin shagunan abokan kasuwanci mu suna kamawa".
"Sai da suka kama mana Mutane 6, munaji muna gani, munbi su zuwa babban Ofishin su dake Kano, wanda wani daga cikin ma'aikatan suka ce sufa umarni daga sama suka samu a cewar sa".
"Bayan munyi duk mai yuyuwa amma aka hanamu belin su, daga Kano kuma sai aka dauki su aka kai su Kaduna, bayan isarmu akace ai ana zargin Æ´an kasuwar mu da yi wa mata "Allurar karin haske bleaching" sannan kuma ana zargin mu da hadawa jarirai man "bleaching" a cewar Ibrahim.
Wanda yace wannan zargi da ake musu babu gaskiya a ciki,
Yakara da cewar daker aka basu belin mutanen su akan miliyoyin kudade.
A don haka yace daga wannan lokaci zuwa yanzu harkokin kasuwancin su ya ja baya sosai, sakamakon ansawa mutane tsoro a wannan kasuwar sabida mutum na cikin hulda da abokan kasuwancin shi jami'an tsaro za su kama shi.
"Muna kira ga Gwamnan Kano da Sarkin Kano da masu ruwa da tsaki da su shiga wanna lamarin, matasa ne ke harkokin kasuwanci a wannan kasuwar, idan aka kashe Kasuwar tabbas Kano zata kara samun baranazar marasa aikin yi." In ji shi